IQNA

Kashedin Jagora Dole Ya Zama Cikin kunnuwanku / Dole A Canja Tsarin Tafiyar Da Hajji

23:29 - October 02, 2015
Lambar Labari: 3377429
Bangaren siyasa, Ayatollah Mowahadi Kermani wanda ya jagoramnci sallar Juma’a ya bayyana cewa dole ne abin da jagora ya fada ya zama a cikin kunnuwan wadanda suka haddasa mutuwar alhazai na kasashen msuulmi kuma dole ne a canja salon tafiyar da aikin hajji.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daya daga cikin na’iban limamin juma’ar birnin Tehran Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Kermani ya bayyana abin da ya faru a Mina da yayi sanadiyyar mutuwar dubban alhazai a matsayin babban abin kunya ga kasar Saudiyya da ba cikin sauki za a iya kawar da shi ba, yana mai kiran da a hukunta wadanda suke da hannu cikin hakan.



Ayatullah Kermani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a a yau din nan a masallacin juma’ar Tehran inda yayin da yake magana kan hadarin da ya faru a Mina a yayin jefar shaidan, ya ce: wajibi ne kasashen musulmi su gudanar da bincike kan hakikanin abin da ya faru yana mai cewa wajibi ne a hukunta wadanda  suke da hannu cikin wannan sakaci da aka yi da yayi sanadiyyar mutuwar alhazan cikin mawuyacin hali.



Na’ibin limamin na Tehran ya kara da cewa abin da ya farun ya tabbatar da rashin cancantar kasar Saudiyya wajen ci gaba da gudanar da ayyukan hajji, don haka wajibi ne a shigo da kasashen musulmi cikin hakan.



Kasashen musulmi daban-daban musamman wadanda suka rasa alhazansu suna ci gaba da nuna damuwa da korafinsu dangane da irin rikon sakainar kashin da mahukuntan Saudiyyan suka yi wa wannan lamarin da yayin sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu hudu.



Kungiyar agaji ta kasar  ta Iran ta sanar da cewa a wani lokaci a yau din nan ne ake sa ran za a fara dawo da kashin farko na gawawwakin alhazan Iran da suka rasu a yayin turmutsutsin Mina gida don yi musu jana’iza da bisne su.



Tashar talabijin din alam da ke watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran ta jiyo babban sakataren kungiyar agajin ta Red Crescent Ali Asgar Ahmadi ya ce an gama dukkanin tsare-tsare da doka ta tanadar wajen dawo da gawawwakin alhazan zuwa gida don yi musu jana’iza da kuma bisne su.



Jami’in ya kara da cewa a halin yanzu dai akwai gawawwakin alhazai 100 da aka gama shirya su ana shirin a taso da su zuwa gida.



A da dai mahukuntan Saudiyya suna ta wasa da hankulan mahukuntan na Iran dangane da batun dawo da gawawwakin alhazan, to sai dai biyo bayan barazanar da Jagoran juyin juya halin Musulunci  yayi a shekaran jiya na cewa Iran za ta mayar da kakkausan martani ga kasar Saudiyya matukar ta ci gaba da wulakanta gawawwakin mahajjatan na Iran, hakan ya tilasta wa mahukutan Saudiyyan ba da hadin kai.



3377354

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha