IQNA

Manufar Makiya Na Yakin Ruwan sanyi Shi Ne Rusa Manufofi Na Juyin Islama

21:23 - October 13, 2015
Lambar Labari: 3385198
Bangaren siyasa, a ganawar da jagoran juyin juya halin muslunci na Iran ya yi tare da shugaban hukumar radiyo da talabijin ta kasar da kuma manyan daraktoci na hukumar ya bayyana cewa dole a zama cikin fadaka domin makiya suna yin amfani da hanyoyin sadarwa wajen hankoron juya manufar juyin Islama.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagora a cikin tarjamar wannan bayani cewa, a  safiyar Litinin ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaba, jami'ai da manyan daraktocin hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran da membobin majalisar sanya ido kan hukumar gidan radiyo da talabijin din, inda yayin da yake karin haske kan manufofin 'makirce-makircen da 'yan mulkin mallaka suke kulla wa tsarin Jamhuriyar Musulunci', ya bayyana kokarin sauya tunani da akidar mutane a matsayin babbar manufar wannan yaki da suka kaddamar kan Iran din. Daga nan sai yayi ishara da irin gagarumar rawar da hukumar gidan radiyo da talabijin ta kasa za ta taka wajen wayar da kan mutane da kuma fada da wannan makircin.



Ayatullah Khamenei ya fara jawabin nasa ne da bayanin irin muhimmancin da hukumar gidan radiyo da talabijin ta kasa take da shi ga tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda yayin da yake ishara da gagarumin yunkurin kafafen watsa labarai da aka samar, Jagoran ya bayyana cewar: Kafafen watsa labarai na kasa suna fagen dagan wannan yaki mai ban mamaki da sarkakiya ne, wanda shi ne wannan fage na yakin kwakwalwa mai matukar muhimmanci da daure kai.



Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kirayi masana masu kishin addini da kasa zuwa ga gagarumin bincike da darasin bangarori daban-daban na wannan yaki na kwakwalwa da ake yi inda ya ce: Manufar da ake son cimmawa a wannan yaki na kwakwalwa ita ce dai wannan manufar da ake son cimmawa a yaki na zahiri, sai dai kawai a wani yanayi mai fadi ne.



Har ila yau Jagoran yayi ishara da wasu sarkakiya da hatsari mai girma da ke tattare da irin wannan yaki na kwakwalwa idan aka kwatanta su da irin wadanda ake da su a yaki na zahiri don haka sai ya ce: Yakin kwakwalwa, sabanin yaki na zahiri na makami, ba abu ne da ake ganinsa a fili ko kuma jinsa a jika ba, kai hatta ma a wasu lokutan ma makiyin zai cutar ba tare da daya bangaren ya fahimta ba.



Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A mafi yawan lokuta yaki na makami ya kan motsa kumajin mutane da samar da hadin kai na kasa. Alhali yaki na kwakwalwa ya kan kawal da kumaji na fada da kuma share fagen haifar da sabani.



Bayan da yayi bayanin hatsarin da ke tattare da yaki na kwakwalwa sama da yaki na zahiri na makami, Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Yakin kwakwalwa ba wai kawai ya takaita kan Iran ba ne, to amma irin na Iran kan wani yaki ne da aka yi darasi da kuma tsara shi da nufin lalata Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sauya ciki da badininta amma tare da kiyaye zahirinta (wato ana ganinta a zahiri, amma a badininta holoko).



Yayin da yake bayanin irin wannan sauyi na badini da ake son yi da cewa shi ne sauya manufa, take da koyarwar da aka sa a gaba, Jagoran ya bayyana cewar: A tsarin irin wannan yaki na kwakwalwa, barin sunan “Jamhuriyar Musulunci” kai hatta ma da kasantuwar wannan malami mai rawani a matsayin jagoranta, ba wani lamari ne mai abin damuwa ba. Abin da ke da muhimmancin shi ne mayar da Iran ta zamanto wata kasa mai lamunce manufofin Amurka, sahyoniyanci da kuma sansanonin ma’abota girman kan duniya.



Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa jami’an gwamnati da sauran al’ummar kasa su ne babbar manufar wannan yaki na kwakwalwa inda ya ce: Dangane da shirye-shiryen da aka kulla wa jami’an gwamnati a wannan yaki na kwakwalwa, nay i magana kan hakan kuma a nan gaba ma zan yi. Amma wadanda ake son cutarwa a wannan yaki na kwakwalwa su ne mutane musamman masana, daliban jami’a, matasa da sauran mutanen da suke motsi da nuna jini a jika.



Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Babban abin da suka sa a gaba shi ne yin tasiri cikin zukatan mutane da sauya abubuwa da dama da suka yi amanna da su musamman matasa da masana, wanda daga cikin wadannan abubuwan da suka yi amanna da su din har da imani na akida ta addini, ta siyasa da kuma al’adu.



Jagoran ya kara da cewa: Mutanenmu suna da imani na akida, musamman na addini, iyali, batun ‘mace da namiji’, ‘yancin kai, fada da ma’abota girman kai, riko da tsarin demokradiyya na Musulunci da sauran batutuwana al’adu. A saboda haka ne makiyan suke kokari wajen ganin sun kashe kaifin wannan imanin da mutane suke da shi ko kuma su kawar da shi.



Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kokarin sauya imanin da mutane suke da shi da tarihinsu a matsayin wata manufa ta daban ta irin wannan yakin inda ya ce: Mutanenmu dai suna da irin mahangarsu dangane da lalatacciyar gwamnatin kama karya da ta gabata a kasar nan, to amma a irin wannan yaki na kwakwalwa kokarin da ake yi shi ne haskaka irin wannan bakin tarihi da mai shi a matsayin wani abu mai kyau.



Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Abin da suke son cimma wajen sauya irin imani da tarihin da ya gabata da ake da shi shi ne nuna wa mutane cewa babu bukatar juyin juya halin Musulunci da aka yi.



Haka nan kuma yayin da yake magana kan kokarin da ake yi na bakanta irin yanayin da ake ciki a halin yanzu, Jagoran cewa yayi: Wadannan mutane suna son su sanya wa matasanmu na yau cewa lalle halin da ake ciki a halin yanzu wani irin yanayi ne abin kunya, sannan kuma babu yadda za a iya kai wa ga ci gaba a irin wannan yanayin, don su sami damar kashe gwiwan matasa da cire musu fata mai kyau.



Jagoran ya bayyana kokarin cusa wa matasa wani irin tunani na karya dangane da yanayin duniya musamman Amurka da Turai da nuna su a matsayin wasu kasashe da suka ci gaba, da ake rayuwa cikin sauki da aminci ba tare da wata matsala ba a matsayin wata manufar ta daban ta irin wannan yaki na kwakwalwa. Daga nan sai ya ce: Babbar manufa kuma ta karshe ta wannan yakin da aka tsara, shi ne haifar da rugujewa ta cikin gida a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar sauya mahangar da kuma raunana imanin da mutane suke da shi musamman ma matasa.



Haka nan kuma yayin da yake ishara da kayan aikin da makiya suke amfani da su a wadannan yakukuwa da suke yi, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Dukkanin irin ci gaban zamani da aka samu a fagagen internet da sauransu ana amfani da su wajen cimma wannan yaki na kwakwalwa ne. Amma mafi muhimmancin irin wadannan kayan aiki shi ne irin dubun dubatan masana da kwararru a bangaren ilimi, siyasa, adabi, zamantakewa da sauran bangarori daban-daban na ilimi wanda duk ake amfani da su wajen cimma manufofin yaki na kwakwalwan.



Jagoran ya bayyana tsare-tsare da aiki da kokari ba kama hannun yaro a matsayin wata siffa da masu tsara irin wannan yaki suke kebanta da ita inda ya ce: Cikin dukkanin fina-finai da rubuce-rubuce da makiyan al’ummar Iran suke yi, babbar manufarsu ita ce cimma manufar wannan yaki na kwakwalwa ko da yake a mafi yawan lokuta ba kai tsaye ba.



A saboda haka ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kokarin yada riko na jeka na yi ka ga addini cikin lamurra da suka shafi dabi’a ta daidaiku da kuma ta zamantakewa a matsayin daya daga cikin boyayyun tsare-tsaren na zamantakewa da kafafen watsa labarai makiya suke tsarawa inda ya ce: Wadannan mutane wajen cimma manufofinsu da gaske suke yi sannan kuma suna da tsare-tsaren da suka yi. To amma a gaskiya mu dai an bar mu a baya a wannan bangaren.



Ayatullah Khamenei ya bayyana irin kokarin da kafafen watsa labarai na gwamnatin Iran suke yi a matsayin wani abin jinjinawa don haka sai ya ce: Wajibi ne a fadada wannan kokari da ake yi su shafi dukkanin bangarori na hukumar gidan radiyo da talabijin, don a janyo hankula masu kallo da saurare kuma su yarda da abin da ake yi.



Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana yin ingantaccen sharhi da kuma la’akari da hakikanin abin da ke gudana a kas a cikin gida, yankin nan da kuma duniya a matsayin aiki mafi muhimmanci wajen cimma manufar kafafen watsa labarai na kasa inda ya ce: irin wannan sharhin zai harhada kwakwala da mahangar bangarori daban-daban na masu gudanarwa a hukumar gidan radiyo da talabijin din da kuma tabbatar da kafafun dukkanin ayyuka.



Haka nan kuma yayin da yake ishara da matsaloli daban-daban da ake fuskanta, yakukuwan basasa hatta da kuma yadda wasu juyin juya hali na zamanin nan suka koma ga yanayin irin gwamnatocin da aka kawar, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wajibi ne a kwatanta matsayin Iran a halin yanzu da matsayin Amurka kimanin shekaru arba’in bayan sanar da ‘yancin kanta ko kuma matsayin Faransa bayan shekaru arba’in da babban juyin juya halin kasar, kafin a iya fahimtar irin gagarumin ci gaban da kasar ta samu.



Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da nauyin da ke wuyan hukumar gidan radiyo da talabijin din wajen wayar da kan al’ummomin duniya dangane da irin bakar farfagandar da makiya suke yi a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.



Kafin jawabin Jagoran sai da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran Dakta Muhammad Sarafraz ya gabatar da jawabinsa inda yayi bayanin ayyukan da aka yi da kuma wadanda aka sa a gaba.





Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gode wa shugaba da sauran manyan daraktoci da kuma ma’aikatan hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran din saboda irin gagarumin kokarin da aiki ba kama hannun yaro da suke yi.



Kafin jawabin Jagoran sai da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran Dakta Muhammad Sarafraz ya gabatar da jawabinsa inda yayi bayanin ayyukan da aka yi da kuma wadanda aka sa a gaba.



3384481

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha