IQNA

Ba Za A Manta Faji’ar Mina Ba / Aikin Jami’ain Diplomasiyya Da Na Ma’aikatar Hajji Ne Su Bi Kadun Lamarin

23:13 - October 20, 2015
Lambar Labari: 3390913
Bangaren siyasa, Jagoran juyin Islama ya yi kakakusar suka dangane da yadda kasashen yammacin turai suka yi gum da bakunansu kana bin da ya faru a Mina, musamman ma masu da’awar kare hakkin bil adama, inda ba za a manta da wannan lamari ba, kuma aikin jami’an diplomasiyya da na ma’aikatar hajji ne su bi kadun wannan batu.

Kamfanin dilalncin labaran iqn aya nakalto daga shafin shafin jagora na yanar gizo cewa, da ranar yau Litinin ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da jami'ai da ma'aikatan da suka kula da ayyukan hajji na bana na Iran inda ya bayyana hadari mai sosa rai da ya faru a Mina yayin aikin hajjin na bana a matsayin daya daga cikin jarrabawa ta Ubangiji. Haka nan kuma yayin da yake sukar irin shirun da gwamnatoci musamman gwamnatocin kasashen yammaci da sauran cibiyoyin da suke ikirarin kare hakkokin bil'adama dangane da wannan babbar musiba ya bayyana cewar: Ko da wasa bai kamata a mance da wannan lamarin ba. Wajibi ne a kan ma'aikatar harkokin waje da hukumar alhazai ta kasa su ci gaba da bin kadin wannan lamarin.
Haka nan kuma a yayin wannan ganawar, yayin da yake ishara da nauyin da ke wuyan gwamnatin Saudiyya dangane da musulmi kimanin dubu bakwai da suka rasa rayukansu yayin wannan hadarin, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Bayan faruwar wannan lamarin, kamata yayi a ji murya guda ta nuna rashin amincewa daga duniyar musulmi. To amma abin bakin cikin shi ne cewa in ban da muryar Jamhuriyar Musulunci ta Iran babu wata muryar da aka ji, hatta gwamnatocin da alhazan kasashensu suna daga cikin wadanda suka rasa rayukan na su. Ba su nuna wani rashin amincewa na a zo a gani ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana ci gaba da bin kadin lamarin da kuma tattaunawa da gwamnatoci da bayanin muhimmancin abin da ya faru da kuma binciko hanyoyin da za a kare sake faruwar hakan a matsayin wani nauyi mai muhimmancin gaske musamman a wuyar ma'aikatar harkokin waje, daga nan sai ya ce: Zahirin abin da ya faru na nuni da cewa hakan ta faru ne sakamakon sakacin gwamnati mai masaukin baki ne. To amma dai koma mene ne wannan dai ba wani lamari ne na siyasa ba, face dai lamari ne da ya shafi dubban musulmi da suke cikin ibada da aiwatar da aikin hajji sannan kuma suka rasa rayukansu alhali suna sanye da harami. A saboda haka wajibi ne a bi lamarin da dukkan karfi.
Jagoran ya bayyana irin gum da bakin da cibiyoyi da hukumomin da suke ikirarin kare hakkokin bil'adama a Turai da Amurka a matsayin wani lamari da ya kamata a yi dubi cikinsa, don haka sai ya ce: Cibiyoyin munafunki da karya masu ikirarin kare hakkokin bil'adama haka nan gwamnatocin kasashen yammaci wadanda a wasu lokuta suke tayar da jijiyoyin wuya a duniya saboda kashe mutum guda, amma sai ga shi sun yi gum da bakunansu don nuna goyon baya ga gwamnatin da suke dasawa da ita.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Idan har da gaske wadannan mutane masu ikirarin kare hakkokin bil'adama suke yi, to da kuwa sun bukaci neman amsa, a biya hasarar da aka haifar, ba da lamunin kare sake faruwar hakan da kuma hukumta wadanda suke da hannu cikin faruwan wannan musibar.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana ci gaba da bin kadin wannan lamarin da kuma ci gaba da kiyaye ambaton wannan lamari mai muhimmanci a matsayin wani nauyi da ke wuyan hukumar kula da ayyukan hajji ta kasar Iran inda ya ce: Bai kamata a yi shiru da kuma barin wannan lamarin ya tafi haka kawai ba. Wajibi ne a ci gaba da gabatar da ci a fage na kasa da kasa har zuwa shekaru masu zuwa; a ci gaba da da gabatar da shi ga gwamnatoci da cibiyoyin da suke ikirarin kare hakkokin bil'adama.
Haka nan kuma yayin da yake mika godiya da jinjinawarsa ga jami'an aikin hajjin na Iran saboda irin hidimar da suka yi musamman irin namijin kokarin da Hujjatul Islam Qadhi Askari (Wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma Amirul Hajji na Iran) da kuma ci gaba da bin lamurra da aiki tukurun da Malam Auhadi (shugaban hukumar alhazai ta kasar Iran) suka yi, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Ko shakka babu ladar wannan namijin kokari yana nan a wajen Allah, kuma hakan shi ne himma da hakuri da kokari a bisa tafarkin Allah wanda Sayyida Zainab (amincin Allah ya tabbata a gare ta) bayan ta ga dukkanin irin wannan bala'i da musiba da ya same su bayan Karbala take cewa, ba su ga komai ba face abu mai kyau.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sai da Hujjatul Islam wal muslimin Qadhi Askari, wakilin Jagora kuma Amirul Hajji na Iran ya gabatar da jawabi da kuma rahoto kan ayyukan da aka gudanar yayin aikin hajjin na bana da kuma matakai da ayyukan da aka gudanar dangane da hadarin da ya faru a Mina din inda ya ce: Wannan hadarin ya faru ne sakamakon mummunan tsarin gudanarwa da nuna rashin ko in kula na jami'an Saudiyya. Don haka bisa hadin gwiwan sauran cibiyoyi mun tattara bayanai kuma za a ci gaba da bin kadin lamarin.
Shi ma a nasa bangaren Malam Auhadi, shugaban hukumar aikin hajji ta Iran yayi karin haske dangane da dawo da gawawwakin alhazan Iran da suka rasa rayukansu gida da kuma kula da wadanda suka sami raunuka inda ya ce: Ana nan ana bin lamarin makomar sauran alhazan Iran da suka rasa rayukansu.
Har ila yau shugaban hukumar alhazan yayi gabatar da rahoto kan aikin hajjin na bana.

 

3389207

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha