IQNA

Jagran juyin Juya Hali ya Aike Da Sako Kan Batun Yarjejeniyar Nukiliya

23:04 - October 21, 2015
Lambar Labari: 3391461
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci ya aike da wani sako zuwa ga shugaban kasa da sauran jami'an kasa kan muhimamncin zama cikin fadaka dangane da batun yarjejeniyar nukiliya da kuma yadda za a fskanci daya bangaren.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, A cikin wata wasikar Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei  da ya aike wa shugaban kasa Hassan rauhani kuma shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Ozma Sayyid Ali Khamenei, yayi ishara da wasu lamurra masu muhimmanci da ya wajaba a lura da su donn kiyaye manufofin kasa yayin aiwatar da yarjejeniyar nukiliya da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya.

Ga dai matanin wasikar kamar haka:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai



Mai Girma Sheikh Ruhani



Shugaban kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuma Shugaban Majalisar Koli Ta Tsaron Kasa

(Allah Ya Kara Masa Nasara)



Bayan gaisuwa da fatan alheri.



A halin yanzu da yarjejeniyar nan da ake kiranta da JPCOA (yarjejeniyar aiki tare kan shirin nukiliyan kasar Iran) ta ketare matakan da doka ta tanadar, bayan gudanar da bincike kanta a majalisar shawarar Musulunci, kwamiti na musamman da sauran kwamitoci (na majalisar) haka nan da kuma majalisar koli ta tsaron kasa, sannan ake jiran in fadi ra’ayina kanta. Don haka a nan ina ganin ya zama wajibi in yi ishara da kuma tunatarwa kan wasu batutuwa don su zamanto hannunka mai sanda a gare ka da kuma sauran jami’an da abin ya shafa kai tsaye ko kuma ta wata hanya ta daban wajen kiyaye manyan manufofi na kasa.



1- Kafin dukkan komai ya zama wajibi ne in mika godiya da jinjinawa ta ga dukkanin wadanda suka taimaka wajen cimma wannan yarjejeniya mai cike da kalubale, a dukkanin zamunna da suka hada da: tawayar masu tattaunawa ta baya-bayan nan wadanda suka yi dukkanin iyakacin kokarinsu wajen bayanin bangarori masu kyau na yarjejeniya da kuma tsayawa kyam wajen ganin an cimma hakan, haka nan da masu suka wadanda suka tunatar da mu bangarorin rauni na wannan yarjejeniyar, haka nan musamman shugaba da membobin kwamiti na musamman na majalisar shawarar Musulunci, da membobi masu girma na majalisar koli ta tsaron kasa, wadanda ta hanyar gabatar da ra’ayoyinsu masu muhimmanci suka sami damar toshe wasu daga cikin gibin da ake da su. Haka nan kuma da shugaba da ‘yan majalisar shawarar Musulunci, wadanda ta hanyar amincewar da ke cike da tsantsan da suka yi ga kudurin da aka gabatar, suka gabatar wa gwamnati ingantacciyar hanyar da ta dace ta aiwatar da wannan yarjejeniyar, haka nan kuma da hukumar gidan radiyo da talabijin ta kasa da marubuta da ‘yan jarida na kasa, wadanda duk da sabanin ra’ayin da suke da shi, amma sun gabatar wa al’umma yanayi na gaba daya na wannan yarjejeniyar. Hakika wannan gagarumin aiki da kokari da tunani cikin lamarin da ake ganinsa a matsayin daya daga cikin batutuwa abin tunawa kana kuma wadanda suke cike da darussa da suka shafi Jamhuriyar Musulunci, lalle abin yabawa da kuma nuna farin ciki ne. A saboda haka da dukkan karfi ana iya cewa lalle wadanda suka taimaka wajen cimma wannan aiki suna da lada na Ubangiji da suka kumshi taimako da rahama da shiriya ta Ubangiji Madaukakin Sarki, insha Allah. Don kuwa alkawarin taimakon Ubangiji ga wanda ya taimaki addininsa, wani alkawari ne da ba zai karya shi ba.



2- Kai din nan da irin tsohon tarihi na shekara da shekaru da kake da shi cikin batutuwan da suka shafi Jamhuriyar Musulunci, don haka ko shakka babu ka san cewa gwamnatin Amurka, cikin lamarin nukiliya ko kuma wani lamari na daban, ba ta taba zama wani abu ba face abokiyar gaba da haifar da matsala (ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran), a nan gaba ma da wuya in ba hakan za ta yi ba. Abubuwan da shugaban Amurka ya fadi cikin wasiku guda biyu da ya aiko min na cewa ba shi da niyyar kifar da (gwamnatin) Jamhuriyar Musulunci, to amma cikin dan karamin lokaci ya tabbatar da rashin gaskiyarsa cikin wannan ikirarin sakamakon goyon bayan da yake yi wa fitina ta cikin gida da kuma taimakon kudin da yake ba wa masu adawa da Jamhuriyar Musulunci. Haka nan kuma irin barazanar kai harin soji – kai hatta ma da barazanar amfani da makaman nukiliya wanda yana iya zama abin da za a kai kararsa kotun kasa da kasa – hakan ya yaye labulen bakar aniyar da shugabannin Amurkan suke da ita. Masana al’amurran siyasa na duniya da mafi yawa daga cikin sauran al’ummomin duniya sun fahimci cewa babban dalilin wannan husuma da gaba maras karewa (da Amurka take nuna wa Iran), shi ne irin yanayi Jamhuriyar Musulunci wanda ya samo asali daga koyarwar juyin juya halin Musulunci. Tsayin daka wajen riko da koyarwar Musulunci na gaskiya na rashin yarda da mulkin mallaka da girman kan (duniya), tsayin daka wajen tinkarar neman wuce gona da iri a kan raunanan al’ummomi, tona asirin irin goyon bayan da Amurka take ba wa ‘yan mulkin mallaka da diran mikiya kan ‘yantattun al’ummomi, goyon baya ba kyafkyaftawa ga al’ummar Palastinu da kungiyoyin gwagwarmaya na kasa, yin Allah wadai da duniya ta yarda da shi kan haramtacciyar kasar Isra’ila, dukkanin wadannan su ne abubuwan da suka sanya Amurka take gaba da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Wannan gabar kuwa za ta ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta sanya Amurka yanke kauna sakamakon irin karfi na cikin gida da take shi.



Irin dabi’a da maganganun gwamnatin Amurka dangane da batun nukiliya da kuma wannan doguwar yarjejeniya, wani abu ne da ke nuni da cewa hakan ma daya ne daga cikin silsilar gaba da kiyayyarsu ga Jamhuriyar Musulunci. Yaudarsu cikin harshen damon da ke cikin maganarsu ta farko wadda ta sanya Iran amincewa da tattaunawa ta kai tsaye ko kuma karya alkawarin da suka saba yi tsawon wannan tattaunawa ta shekara biyu ko kuma bukatar gwamnatin Sahyoniyawa da diplomasiyyarsu ta son amfani da karfi da tursasawa a kan gwamnatoci da cibiyoyin Turai da suke cikin tattaunawar, dukkanin wadannan abubuwa ne da suke nuni da cewa da manufa ta yaudara Amurka ta shiga wannan tattaunawar ta nukiliya, ba wai da niyyar magance matsalar cikin adalci ba, face dai da niyyar cimma manufofinsu ta kiyayya a kan Jamhuriyar Musulunci.



Ko shakka babu taka tsantsan da aka nuna dangane da bakar aniyar gwamnatin Amurka sannan da kuma irin tsayin dakan da jami’an Jamhuriyar Musulunci suka yi tsawon zamanin tattaunawar nan, lalle hakan ya samu damar hana cutarwa da dama da za a iya fuskanta.



A halin yanzu da aka kai ga gacin wannan tattaunawar ta hanyar cimma wannan yarjejeniyar ta JPCOA, akwai wasu gibi da ake da su a bangarori daban-daban, wadanda idan ba a sanya ido sosai ba, za a iya fuskantar hasarori masu girma ga kasar nan a yanzu da kuma nan gaba.



3- Bangarori guda tara da doka ta baya-bayan nan da majalisar ta kafa da kuma ra’ayin majalisar koli ta tsaron kasa mai kumshe da bangarori goma, sun kumshi wasu batutuwa masu amfani da kuma tasiri da wajibi ne a kula da su. Ala kulli hal, duk da hakan akwai wasu batutuwa na daban da suke tafiya tare da wadancan da suka zo cikin wadancan kudururruka biyu, da zan ambace su.



Na farko: Bisa la’akari da cewa Iran ta amince da wannan tattaunawar ce saboda dauke mata takunkumin zalunci na tattalin arziki da aka dora mata da kuma cewa a cikin wannan yarjejeniyar da aka cimma an tsayar da cewa za a dage takunkumin ne bayan Iran ta aikata nauyin da ke kanta. A saboda haka wajibi ne a dau matakai masu karfi da za su lamunce rashin saba abin da aka cimma din daga daya bangaren, wanda daga cikin su har da sanarwa a rubuce daga bangaren shugaban Amurka da Tarayyar Turai na dage wadannan takunkumin. Wajibi ne cikin wannan sanarwar ta Tarayyar Turai da shugaban kasar Amurka a fili a fadi cewa za a dage wadannan takunkumin ne gaba daya. Duk wata magana ta cewa tushen takunkumin zai ci gaba da zama, yana a matsayin karen tsaye ga yarjejeniyar da aka cimma ne.



Na Biyu: Tsawon wadannan shekarun takwas (din da aka tsayar), sanya duk wani irin takunkumi a kowane bangare ne ta hanyar fakewa da wani abu na daban (ciki kuwa har da tsararrun abubuwan da suka saba fakewa da su irin su ta’addanci da take hakkokin bil’adama), a bangaren kowane guda daga cikin kasashen da aka tattauna da su din. To za a dauki hakan a matsayin karya wannan yarjejeniyar, sannan kuma wajibi a kan gwamnati, bisa sashi na uku na kudurin majalisa, ta yi abin da ya dace sannan kuma ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar.



Na Uku: Abubuwan da suka zo cikin sashin da ya biyo baya, za a aiwatar da su ne kawai a lokacin da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta sanar da kawo karshen batun cewa akwai yiyuwar Iran tana shirin kera makaman nukiliyan (PMD).



Na Hudu: Za’a fara aiwatar da abubuwan da suka shafi sabunta cibiyar (nukiliya) ta (garin) Arak da kuma kiyaye ayyukan da ake yi a wajen ne kawai a lokacin da aka kulla yarjejeniyar da babu kokwanto cikinta dangane da gabatar da makwafin hakan da kuma samun cikakken lamuni aiwatar da hakan.



Na Biyar: Za’a fara aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma dangane da musayen taceccen uranium da ake da shi da kuma batun ‘Yellow Cake” da wata kasa ta waje ne kawai bayan an kulla wata yarjejeniyar aiki da babu kokwanto cikinta bugu da kari kan samun cikakken lamuni. Wajibi ne wannan musayen da aka ambata ta zamanto a hankali a hankali sannan kuma a matakai daban-daban.



Na Shida: Daidai da dokar da majalisa ta kafa, wajibi ne a tsara da kuma share fagen da ya wajaba wajen fadada masana’antar makamashin nukiliya na matsakaicin zango da ya hada da tafarki na ci gaba a lokuta mabanbanta tun daga yanzu har zuwa shekaru 15 masu zuwa da zai kai ga samun dubu 190 na wuta, a tsara hakan da kuma gabatar da shi ga majalisar koli ta tsaron kasa don tattaunawa kansa. Wajibi ne wannan tsarin ya zamanto ya goge duk wata damuwar da ake da ita biyo bayan wasu bukatu da suka zo cikin wancan yarjejeniyar ta nukiliyan.



Na Bakwai: Wajibi ne hukumar kula da makamashin nukiliya (ta Iran) ta ci gaba da gudanar da bincike da fadada fasahar (nukiliyan) a bangarori daban-daban ta yadda bayan shekaru takwas din nan ba za a fuskanci komai kashin rashi a bangaren tace sinadarin uranium da aka yarda da shi cikin wannan yarjejeniyar ba.



Na Takwas: Wajibi ne a san cewa a duk lokacin da aka fuskanci rashin fahimta cikin yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma, ba za a amince da fassarar daya bangaren da ake fuskanta ba. Mizani kawai shi ne matanin yarjejeniyar.



Na Tara: Bisa la’akari da irin sarkakiyar da duhun da ke cikin matanin wannan yarjejeniyar, haka nan kuma da tunanin karya alkawari da yaudarar daga daya bangaren musamman Amurka, hakan ya wajabta samar da wani kwamitin mai karfin gaske don sanya ido kan ci gaban da aka samu da kuma tabbatar da cewa daya bangaren bai karya alkawarin da ya dauka ba da kuma cimma abubuwan da aka fadi a sama. A majalisar koli ta tsaron kasa ne za a tattaunawa da kuma tsara yadda kwamitin zai kasance da kuma aikinsa.



Bisa la’akari da abubuwan da aka ambata, na amince da kudurin da aka cimma a zaman a 634 na majalisar koli ta tsaron kasa da aka gudanar a ranar 19/05/1394 tare da kiyaye abubuwan da na ambata a sama.



Daga karshe, kamar yadda na tunatar a tarurruka daban-daban da na yi da kai da sauran jami’an gwamnati, haka nan da kuma abubuwan da na fadi a ganawa daban-daban da al’ummarmu abin kauna, dage takunkumin (da aka sanya mana), duk da cewa wani aiki na wajibi ne wajen dage zalunci da tabbatar da hakkin al’ummar Iran, to amma ba za a iya karfafa tattalin arziki da kyautata yanayin rayuwar al’umma da maganin matsalolin da ake fuskanta in ba ta hanyar riko da dukkan karfi da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai ba. Fatan da nake da shi ne za a ci gaba da bin wannan lamari da dukkan karfi musamman wajen karfafa irin abubuwan da ake samarwa a cikin gida, da kuma yin taka tsantsan wajen ganin ba a bude fagen shigo da kayayyakin waje daga lokacin da aka dage takunkumi ba, musamman shigo da kayayyakin da ake kera su a Amurka ba. Lalle a nesanci hakan.



Ina roka maka da sauran jami’an gwamnati nasara da taimako daga wajen Allah Madaukakin Sarki.



Sayyid Ali Khamenei



29, Watan Mehr, 1394.



3391256



 



 

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha