IQNA

Jagoran Juyin Islama:

Masallacin Wuri Ne Na Yada Koyarwar Addinin Muslunci Da Al'adunsa

23:55 - August 23, 2016
Lambar Labari: 3480736
Bangaren siyasa, a lokacin da yake zantawa da malamai da kuma limamai na birnin Tehran da kewaye, jagoran juyin juyin juya halin muslunci a Iran ya bayyana irin matsayin da masalalci yake da shi a acikin addinin musulunci da yada koyarwarsa acikin jama'a.

Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a safiyar yau Lahadi (21-08-2016) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da limaman masallatan lardin Tehran inda ya bayyana masallaci a matsayin wata cibiya ta "zamantakewa, neman shawara, tsari da yunkuri na zamantakewa da al'adu. Har ila yau kuma yayin da yake ishara da wajibcin karfafa imanin mutane a matsayinsu na abin dogaro na asali na juyin juya halin Musulunci da kuma tsarin Musulunci na kasar Iran ya bayyana cewar: Wajibi ne a yi a ba da muhimmanci ga lamurra da suka shafi al'adu don ayyana irin nauyin da ke wuyanmmu dangane da batutuwan da suke faruwa.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan dalilan ayyana ranar ta duniya ta masallatai, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta amince da wannan rana (a matsayin ranar duniya ta masallatai) ne sakamakon matsin lambar Jamhuriyar Musulunci ta Iran saboda sanya wuta da sahyoniyawa suka yi wa masallacin Kudus don share wa al'ummar musulmi fagen fada da haramtacciyar kasar Isra'ila. A saboda haka wajibi ne a ci gaba da kallon lamarin da wannan mahangar.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kafa masallaci a matsayin wani tsari na addinin Musulunci da nufin samar da fagen tattaunawa da kulla alaka ta zamantakewa da 'ambaton Allah da salla da kuma tunawa da Ubangiji' don haka sai ya ce: A tarihin Musulunci, masallaci ya kasance wata cibiya ce ta yin shawarwari, aiki tare da daukar matsayi dangane da batutuwa masu muhimmanci na zamantakewa, siyasa da aikin soji.

Don haka ne sai Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da muhimmancin da ke tattare da 'salla' inda ya ce: Wajibi ne salla ta kasance cikin tsari da kuma mika kai ga Allah Madaukakin Sarki sannan kuma da nesantar abubuwa masu cutarwa irin su gafala da riya. Rayar da limamai za su taka kuwa wajen bayani da kwadaitar da salla a aikace wata rawa ce mai matukar muhimmanci.

Jagoran ya bayyana masallaci a matsayin wani sansani na dukkanin ayyukan alheri don haka sai ya ce: Wajibi ne masallaci ya zamanto wani sansani na "gina mutum, gina zuciya da kuma duniya, fada da makiya, samar da basira da kuma share fagen samar da ci gaba na Musulunci'. A saboda haka, nauyin da ke wuyan limami, baya ga batun jagorantar salla,har da tsayar da gaskiya, bayanin addini da kuma sanar da hukunce-hukunce na addini.

Ayatullah Khamenei ya bayyana limami a matsayin a tushen masallaci don haka sai ya ce: limancin salla wani aiki ne mai muhimmancin gaske, a saboda haka bai kamata a kalle shi a matsayin wani aiki na gefe ba. A saboda haka wajibi ne gudanar da shi yadda ya kamata ta hanyar kasantuwa cikin tsari cikin kwanciyar hankali a masallacin da ba da cikin tsinuwa da kuma tattaunawa da mutane da tsara zama don amsa tambayoyin da matasa suke da su.

Jagoran ya bayyana ba wa masallacin muhimmanci a matsayin daya daga cikin abubuwan da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya ba su muhimmanci tun ranakun farko-farko na nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran inda ya ce: masallaci dai wata cibiya ce ta gudanar da ayyuka na zamantakewar al'umma sannan kuma wajen karfafa tunani da kwadaitar da mutane zuwa ga ayyuka daban-daban na zamantakewa.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana masallaci a matsayin wata cibiya ta tsayin daka da kuma fada da kokarin lalata al'adun jama'a yana mai cewa: matukar dai aka rasa tushe na al'adu a tsakanin al'umma,to kuwa an rasa dukkan komai.

Jagoran ya bayyana cewar a farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran makiya sun kara kaimi wajen kutse cikin al'adun jama'a da nufin lalata su inda ya ce: Babbar manufar wannan gagarumin aiki shi ne cutar da imani na addini da mutane suke da shi, wato wannan lamarin da shi ne tushen nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma kafa Jamhuriyar Musulunci a kasar Iran.

Ayatullah Khamenei ya bayyana juyin juya halin Musulunci a matsayin wata girgizar kasa ga tushen 'yan mulkin mallaka inda ya ce: Albarkacin Musulunci ma'abocin juyi da kuma "juyin juya halin Musulunci" masu tinkaho da karfi sun gaza wajen cimma manufarsu wacce ita ce mulkin mallaka a yankin nan. A halin yanzu dai Amurka tana cikin tsaka mai wuya a yankin yammacin Asiya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Idan da ba don imani da riko da koyarwar Musulunci na mutane ba, to da kuwakasar Iran tamkar sauran kasashe da ta zamanto karkashin ikon Amurka da wasun Amurkan. A saboda haka ne suke fada da kuma kokari wajen ganin sun lalata wannan imani na mutane.

Jagoran ya bayyana matasa a matsayin babban abin da makiya din suka sa a gaba wajen ganin sun lalata musu dabi'u da kuma raunana imanin da suke da shi, sai dai ya ce: Duk da irin wadannan makirce-makirce, to amma wani adadi mai yawan gaske na matasan sun kasance wata babbar mu'ujiza ta wannan juyin, sannan matasan yanzu suna a sahun gaba fiye da matasan farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci.

Ayatullah Khamenei ya bayyana irin rawan da masallatai za su taka wajen kara irin tsayin daka da fada da kokarin lalata al'adun mutane a matsayin wata rawa mai muhimmancin gaske don haka ya bayyana masallacin a matsayin: "wata cibiya mai girma ta tattaro jama'a da yunkuri na kyautata al'adun jama'a.

Jagoran ya kirayi limaman masallatan zuwa ga amfani da ingantattun salo a masallatan irin su zama tare da mutane a matsayin wata hanya ta isar da sako wanda kuma hakan wani lamari ne mai tasirin gaske.

Haka nan yayin da yake bayanin wani batu mai muhimmancin gaske, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana al'adu da basira a matsayin wasu lamurra masu muhimmanci cikin ayyuka na siyasa inda ya ce: Ma'anar siyasa ta hakika ba ita ce goyon bayan wannan mutumin ko wancan mutumin ba, face dai siyasa tana nufin mahanga mai kyau sannan da kuma karfin yin sharhi da fahimtar yunkuri na hakika na al'umma.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: A mahangar ta hakika ta siyasa, wajibi ne a yi dubi cikin yunkuri da dabi'un al'umma, sannan kuma a samar da amsoshin tambayoyin da ake gabatarwa da kuma inda aka dosa, shin an kama hanyar tabbatar da adalci na zamantakewa, 'yanci na hakika da kuma tabbatar da ci gaba na Musulunci ne ko kuma mun kama hanyar dogaro da Amurka da tasirantuwa da abubuwan da kasashen yammaci suka tsara mana?

Jagoran ya ce a irin wannan yanayin ne za a iya gane inda mutum, kungiya ko kuma jam'iyya ta siyasa ta sa gaba.

Yayin da yake ba da misali kan muhimmancin da ke cikin samun mahanga da kuma yin sharhin da ya dace wa lamurra, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: A farko-farkon fitinar da ta faru a shekara ta 2009 (bayan zaben shugaban kasa) na gaya wa daya daga cikin jagororin wannan fitinar cewa a zahiri kana tare da wannan tsari sannan kuma kamar yadda ka fadi kana nuna rashin amincewarka ne da sakamakon zaben, to amma ka san cewa jagorancin wannan lamarin zai fada hannun 'yan kasashen waje ne, su kuma za su yi amfani da wannan aiki na ku wajen cutar da asalin wannan tsari da gwamnati ta Musulunci.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wadannan mutanen ba su fahimci hakikanin wannan magana ta zabe ba kuma kowa ya ga yadda aka yi amfani da batun zaben wajen cutar da tushen wannan tsarin.

A wasu bangarori na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin haske dangane da muhimmancin tsai da salla da kuma ba da muhimmanci ga matasa da kuma karfafa imaninsu.

A karshen jawabin nasa Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Duk da irin wannan gagarumar kiyayya da ake nuna wa tsarin Musulunci na Iran a fili da a boye, to amma duk da haka wannan kalma mai kyau ta Jamhuriyar Musulunci a kullum sai kara karfi da daukaka take yi, sannan kuma albarkacin imani da hadin kan al'umma har ya zuwa yanzu wannan makirci ya sha kashi.

Kafin jawabin Jagoran sai da Hujjatul Islam wal muslimin Haj Ali Akbari, shugaban cibiyar kula da lamurran masallatai ya gabatar da jawabinsa da kuma rahoto kan irin ayyukan da cibiyar tasa ta gudanar.

3524358



Abubuwan Da Ya Shafa: iqna jagora ayatullah sayyid ali khamenei
captcha