IQNA

Zaman Makokin Shahadar Fatima (SA) A Ingila Da Sweden

23:20 - March 02, 2017
Lambar Labari: 3481276
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da zaman makoki na shahadar Sayyida Fatima Zahra (SA) a kasashen Birtaniya da kuma Sweden.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin ic-el.com cewa, ana gudanar da zaman makokin shahadar Sayyida Zahra (SA) a birnin London a cibiyar muslucnci da ke birnin.

Ana gudanar da bayanai da kuma juyayi kan shahadarta, gami da irin darussan da za aiya dauka daga rayuwarta mai albarka, kasantuwarta ita ce diyar manzon Allah da ta rayu da shi kuma yake sanar da ita sirrika na rayuwa da addini.

A can birnin Stockholm na kasar Sweden ma an gudanar da irin wannan zaman taro na tunawa da zagayowar lokacin shgahadar Fatima Zahra (SA) a babbar cibiyar muslunci ta Imam Ali (AS) da ke birnin.

Inda a ka gabatar da jawabai da kuma wakoki da suka shafi juyayi na shahadarta, tare da bayar da abincin dare ga dukanin mahalarta.

Malam Bahmanpour shi ne yake gabatar da jawabi a wurin, inda yake tunatar da musulmin da suka taru wurin matsayin Sayyida Zahra (SA) da kuma iyalan gidan amnzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.

3579711


captcha