Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne jami'an gwamnati su yi la'akari da abubuwa uku, na farko yanayin tattalin arziki da yanayin rayuwar mutane, sannan su yi kokari wajen kyautata alakarsu da sauran kasashen duniya, na uku kuma su tsaya kyam wajen tinkarar girman kan ma'abota girman kan duniya.
A safiyar yau ne dai ne aka gudanar da bikin tabbatar da shugaba Ruhanin a karo na biyu na shugabancinsa. A bisa kundin tsarin mulkin Iran duk shugaban kasa da aka zaba yana bukatar amincewar Jagoran juyin juya halin Musulunci kafin yayi rantsuwar kama aiki a gaban majalisar dokokin kasar.
Shi ma anasa bangaren shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar ko da wasa Iran ba za ta taba mika kai da kuma yarda da kokarin da makiya suke yi na mai she ta saniyar ware a tsakankanin kasashen duniya ba.
Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a wajen bikintabbatar da zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasar Iran karo na 12 da aka gudanar a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci lalle abin alfahari ne a ga al'ummar Iran da suka sami kansu karkashin inuwar tsarin Jamhuriyar Musulunci.
Yayin da yake magana kan zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar Iran a baya inda aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a wa'adin mulki na biyu, shugaba Ruhani ya ce hakan yana nuni da tsarin demokaradiyya na addini da ke iko a kasar Iran inda jama'a suke da bakin fadi cikin gudanar da kasa, yana mai alkawarin kare hakkokin al'umma da kasar Iran daga duk wani kokarin wuce gona da iri na makiya.
A ranar Asabar mai zuwa ce ake sa ran shugaba Ruhanin zai yi rantsuwar kama aiki a gaban 'yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran da ake sa ran shugabanni da manyan jami'an kasashe da dama na duniya za su halarta.