Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne gobara ta kama a babbar cibiyar Darul kur’an da ke birnin Kirawan na kasar Tunisia amma daga bisani ‘yan kwana-kwana sun samu nasarar kasha gobarar.
Rahoton ya ce gbarar ta yi sanadiyyar konewar wasu daga cikin kayayyakin da suke a cikin cibiyar.
Daga cikin kayan da suka kone har da ittafai da kuma da kuma wasu kayan cibiyar da suka hada da kujeru da kuma dakin daukar shirye-shirye wato studio.
Wannan cibiya dai it ace cibiyar kur’ani mafi girma akasar Tunisia, kamar yadda kuma tana daga cikin manyan cibiyoyin kur’ani masu tarihi a nahiyar Afirka.