IQNA

Majalisar Dokokin Iran Ta Yi Allawadai da Takunkuman Amurka A Kan Jami’atul Mustafa

22:56 - December 27, 2020
Lambar Labari: 3485497
Tehran (IQNA) majalisar dokokin Iran ta yi Allawadai da kakkausar murya a kan takunkuman da Amurka ta dora wa jamimi’atul Mustafa.

A wani bayani da dan majalisa Ruhullah Mutafakkir Azad ya karanta ya bayyana cewa; makiyan ci gaban ilimi sun sake nuna kansu a wannan lokaci, ta hanyar kai farmaki akan cibiya mai girma irin jami’ar Mustafah, wacce tana daya daga cikin muhimman cibiyoyin ilimi na duniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa; Wannan irin matakin yana nuni ne da gajiyawar Amurka da yanke kaunarta akan ci gaban ilimi da al’ummar Iran take yi.

A makon da shude ne dai Baitul-malin Amurka ya sanar da kakaba takunkumi akan jami’ar Mustafa.

3943649

 

 

captcha