IQNA

Sayyid Safiyuddin: Gushewar Amurka A Gabas Ta Tsakiya Za Ta Kawo Babban Sauyi A duniyar Musulmi

20:54 - October 04, 2021
Lambar Labari: 3486387
Tehran (IQNA) shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar Hizbullah Sayyid safiyuddin ya bayyana cewa, Amurka tana kan hanyar gushewa a gabas ta tsakiya.

A cikin wani bayaninsa shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar Hizbullah Sayyid safiyuddin ya bayyana cewa, Amurka tana kan hanyar gushewa a gabas ta tsakiya, kuma hakan zai kawo gagarumin sauyi a duniyar musulmi.
Yace sauye-sauyen da ake samua  cikin siyasar Amurka suna nuni da raunin da kasar take yi a fagen siyasar duniya, wanda kuma hakan bababr izna ce ga kasashen larabawa wadanda suka dogara da Amurka bisa zaton cewa ita ce kawai za ta iya kare musu kujerunsu an saurata domin su tabbata a kan mulki.
 
Dangane da matsalolin makamashi da kasar Lebanon ta shiga kuwa, ya bayyana cewa Hizbullah ta  shigo da makamashi daga kasar Iran zuwa Lebanon ne don fitar da kasar daga dimbin matsalolin da take fuskanta.
 
Shugaban majalisar koli ta zartawrwa ta kungiyar Sayyid Hashim Safiyuddin ya bayyana haka a jiya da yamma a wani taron da ya halarta a garin Bint-Jbeil daga kudancin kasar.
 
Safiyuddin ya kara da cewa, ya san cewa wasu 'yan kasar Lebanon suna jin tsoron manyan kasashen duniya, amma shigo da makamashi daga kasar Iran ya bayyana gazawar haramtacciyar kasar Isra’ila wajen hana makashin isa kasar Lebanon daga kasar Iran.
 
Ya kuma kara da cewa duk wani zabin da kasar Lebanon zata yi matukar ba ta nuna 'yancinta ba, mika kai ne ga bukatun Isra'ila a yankin.
 
Don haka banda shigo da makamashi daga kasar Iran akwai wasu shirye-shiryen wanda kungiyar take da su don tabbatar da 'yancin kasar Lebanon da kuma fitar da ita daga mummunan halin da aka jefata ciki.
captcha