Kassim al-Araji, shugaban majalisar tsaron kasa a Iraki ya sanar a hukumance cewa an kawo karshen yakin da dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta a Iraki da yammacin yau.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa a yau Alhamis, a zagaye na karshe na tattaunawa da jami'an kawancen kasashen duniya da aka fara a bara, a hukumance mun sanar da kawo karshen aikin soji da kuma ficewarsu daga Iraki.
Ya kara da cewa: Daga yanzu za a ci gaba da hulda da dakarun hadin gwiwa a fagen ba da shawarwari, horarwa da karfafa gwiwa.
A ranar 5 ga Janairu, 2020, kwanaki biyu bayan kisan Qassem Soleimani da al-Mohandes, majalisar dokokin Iraki, ta amince da korar sojojin Amurka tare da ayyana ta a matsayin doka.
https://iqna.ir/fa/news/4019727