IQNA

Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Zagayowar Ranakun nasar Juyin Iran

22:08 - February 10, 2022
Lambar Labari: 3486935
Teran (IQNA) A cikin sakon da shugaban majalisar dokokin kasar Labanon Nabih Birri ya fitar ya taya Jagoran juyin juya halin Musulunci murnar cika shekaru 43 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran.

Sakon yana cewa: Shekaru 43 kenan da fara samun kwanciyar hankali, annuri, karfi a dukkanin bangarori a kasar Iran,  duk wannan ya samo asali ne daga falalar nasarar juyin juya halin Musulunci da marigayi Imam Ruhollah Musawi Khumaini ya yi, tare da irin jagoranci na hikima.

Ya kara da cewa: A wannan lokaci mai albarka, ina mai farin cikin taya ku da al'ummar Iran murna a madadin kaina da na majalisar dokokin kasar Labanon.

A cikin wannan sakon, shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon ya kuma taya shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran Ibrahim Raisi da kuma shugaban majalisar shawarar musulunci Dr Muhammad Baqer Qalibaf murna.

 

4035308

 

captcha