IQNA

Aljeriya: Za Mu Ci Gaba Da Goyon Bayan Falastinu Har Sai An Kawo Karshen Mulkin Mallaka

19:59 - April 24, 2022
Lambar Labari: 3487210
Tehran (IQNA) shugaban kasar Aljeriya ya bayyana cewa suna goyon bayan falastinu har cikin zuciyarsu saboda 'yan adamtaka da kuma kiyayya da zaluncin 'yan mulkin mallaka

Tebboune ya jaddada cewa, Aljeriya ba za ta yi watsi da Falasdinu ko yankin Yammacin Sahara ba, domin batutuwa ne na kawar da mulkin mallaka.

Ya ci gaba da cewa, "Algeria kasa ce mai karfi a kungiyar 'yan-ba-ruwanmu, saboda haka dukkanin matakanta matakai ne da suka dace da kundin tsarin mulki da kuam siyasart ata kasa da kasa.

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya bayyana matakin da firaministan kasar Spain ya dauka, na goyon bayan kudirin kasar Morocco kan yammacin Sahara, yana mai cewa, “hakika ba abu ne da ba za a amince da shi ba.

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya tabbatar da cewa alakar Aljeriya da Rasha ta dade tun shekaru 60 da suka gabata.

Ya kara da cewa, akwai batutuwa da dama da suke tasowa amma dole ne mu tabbatar da matsayinmu da kuma matsayin alakarmu da Rasha, kan cewa alaka ce ta tarihi, wadda ba za ta taba girgiza sakamakon matsin lamba ba.

Ya ci gaba da cewa Rasha kasa ce abokiyar Aljeriya, saboda haka alakarsu na nan daram, kamar yadda kuma alakarsu da Amurka ma tana nan a irin yanayinta.

 

4051965

 

 

captcha