IQNA

Wani Matashi Bafalastine Ya Yi Shahada Bayan Da Sojojin Isra’ila Suka Harbe Shi Da Bindiga

13:28 - October 13, 2022
Lambar Labari: 3488002
Tehran (IQNA) Sojin Isra’ila sun kai samame a yankunan Falastinawa da ke gabar yammacin kogin Jordan a jiya Laraba.

A jiya Laraba Sojin Isra’ila sun kai samame a yankunan Falastinawa da ke gabar yammacin kogin Jordan, inda suka yi ta harbe-harbe da  bindigogi da kuma harba hayaki mai sanya hawaye a kan gidajen jama’a.

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana cewa, sojojin Isra’ila sun kashe wani matashi bafalastine mai suna  Usama Mahmoud Adawi dan shekaru 18, wanda harsasai da dama suka harba a cikin cikinsa a lokacin kazamin fada da aka yi a sansanin 'yan gudun hijira na al-Arroub, a cewar kamfanin dillancin labaran Wafa.

Rahotanni sun ce an kai matashin zuwa wani asibiti da ke kusa domin duba lafiyarsa, amma ya mutu bayan isowarsa.

A wani wurin kuma a birnin Ramallah da ke tsakiyar gabar yammacin kogin Jordan, an kwantar da wasu Falasdinawa biyu a rukunin likitocin Falasdinu. Daya daga cikin su ya samu munanan raunuka a kirjinsa, bayan da sojojin Isra’ila suka kai musu hari.

 

4091511

 

captcha