IQNA

Zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Al-Khalifa a Bahrain

14:12 - November 06, 2022
Lambar Labari: 3488131
Tehran (IQNA) An gudanar da zanga-zangar nuna adawa da zaben 'yan majalisar dokoki na bogi, da daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawan da kuma sakin fursunonin siyasa a Bahrain.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, yayin da ya rage mako guda a gudanar da zabe a kasar Bahrain, an gudanar da zanga-zangar nuna adawa da zaben ‘yan majalisar dokoki na bogi, da daidaita alaka da gwamnatin yahudawan sahyoniya, da kuma sakin fursunonin siyasa.

Wannan zanga-zangar ta gudana ne a yayin da Paparoma Francis shugaban mabiya darikar Katolika na duniya ya je Bahrain domin halartar taron zaman lafiya da zaman tare.

4097274

 

 

 

captcha