IQNA

An yi maraba da matakin da Majalisar Dinkin Duniya na yin Allah wadai da kona kur'ani

15:28 - July 14, 2023
Lambar Labari: 3489467
Jeddah (IQNA) Kungiyar kasashen musulmi, Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa sun yi maraba da matakin da hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta dauka na amincewa da kudurin majalisar na yin Allah wadai da wulakanta litattafai masu tsarki da kuma rashin yarda da addini.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CNN cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi maraba da amincewa da kudurin kwamitin kare hakkin bil’adama na majalisar dinkin duniya da nufin karfafa yunkurin hadin gwiwa na yin watsi da tozarta litattafai masu tsarki da kuma rashin yarda da addini.

An amince da kudurin "Yaki da kiyayyar addini da ta kunshi tunzura wariya, gaba ko tashin hankali" a zaman taron Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam karo na 53 bisa bukatar kungiyar kasashen musulmi a Geneva.

An dauki wannan matakin ne a matsayin mayar da martani ga tada hankali da wulakanta kur'ani mai tsarki da aka yi a wasu kasashen turai da wasu kasashen duniya.

Har ila yau kasar Saudiyya ta fitar da sanarwar da aka buga a kamfanin dillancin labaran kasar, inda ta jaddada cewa: Wannan mataki na hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya faru bayan bukatar kasashen musulmi da dama, wani lamari ne na ka'idojin mutuntawa. addinai da al'adu daban-daban, da kuma inganta dabi'un dan Adam, an tabbatar da su a cikin dokokin kasa da kasa.

A ranar Talata ne hukumar kare hakkin dan Adam ta zartas da wani kuduri mai kakkausar murya na yin Allah wadai da duk wani yunkuri ko nuna kyamar addini, gami da tozarta kur’ani mai tsarki a bainar jama’a.

Majalisar ta amince da kuduri mai taken "Yaki da kiyayyar addini da ke da alaka da nuna wariya, gaba ko tashin hankali".

Har ila yau Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi marhabin da wannan mataki na Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya na yaki da kyamar addini, wanda ya kunshi tunzura wariya, gaba ko tashin hankali, tare da jaddada wajibcin mutunta addinai, hakuri da zaman lafiya a matsayin ka'idojin hanya mafi inganci. 

 

4154947

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: inganci maraba da hakkoki dan adam addini
captcha