IQNA

Musulmi sun fusata kan hukuncin da kotun kolin Kenya ta yanke mai cike da cece-kuce

15:49 - August 20, 2023
Lambar Labari: 3489673
Nairobi (IQNA) Hukuncin da kotun kolin kasar Kenya ta yanke game da bayar da lasisin yin rajistar kungiyoyin 'yan luwadi a kasar ya haifar da rashin gamsuwa sosai a tsakanin musulmi.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, kwamitin masallacin Jamia na birnin Nairobi a madadin al’ummar musulmi ya fitar da sanarwar manema labarai tare da bayyana cewa wannan hukunci abu ne mai ban tsoro da bai dace ba kuma sam ba za a amince da shi ba.

Sanarwar ta nuna damuwarta kan manufofin Kenya na tallafawa 'yan luwadi da madigo da sauran kungiyoyin da ba su dace ba.

Shi ma Abdulbari Hameed limamin masallacin Jama Masjid na Musulman Nairobi ya ce dangane da haka: hukuncin da kotun kolin Kenya ta yanke zai yi illa ga al'adun addini da al'adu da iyali a wannan kasa. Wadannan alakoki na dabi'a sun yi mulkin al'ummar Kenya tsawon shekaru aru-aru tare da kafa tushen dangantakar zamantakewar wannan kasa. Yawancin mutane a Kenya suna bin addinin Kiristanci, Musulunci da akidar gargajiya. Babban abin da ke tattare da wadannan mutane shi ne adawa da luwadi da madigo a matsayin aikin fasikanci da laifi kuma ba za a iya lamunta da wannan batu a cikin al'ummar Kenya ba.

Al'ummar musulmin dai sun sha alwashin yin tir da hukuncin, tare da yin kira ga 'yan majalisar dokokin kasar da su bullo da wasu kwararan dokoki domin ci gaba da aikata laifukan alaka tsakanin jinsi guda.

 

4163488

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: alaka laifuka aikata dokoki majalisar dokoki
captcha