IQNA

Nuna manyan hotunan kur'ani mai girma a tsakanin hubbarori biyu na Karbala

16:04 - September 05, 2023
Lambar Labari: 3489764
Karbala (IQNA) Daya daga cikin tawagogin masu tatakin Arbaeen a Iraki sun nuna manya-manyan hotunan kur'ani mai tsarki a lokacin da suke shiga hubbaren Imam Hussain (AS)

A cewar Al-Sumariyeh, jerin gwanon  Bani Amer sun nuna manya-manyan hotunan kur'ani mai tsarki a lokacin da suke shiga birnin Karbala da kuma Hubbare.

A bisa hotuna da faifan muzaharar da maukibin Bani Amer daga lardin Basra ya wallafa, wannan jerin gwano  ta shirya wani shiri na musamman na kara daukaka sunan kur’ani mai tsarki a Karbala.

Jerin gwanon maukibin Bani Amer dai na daya daga cikin jerin gwanon Husaini mafi girma a duniya, inda a duk shekara ake rera taken addini da na kur'ani a yayin gudanar da tarukan  Arba'in a hubbaren Iamm Hussain (AS), kuma a wannan shekara ta nuna irin ayyukan da ta yi ta hanyar nuna manyan hotunan kur'ani.

Wannan mataki na jerin gwanon Maukibin Bani Amer na mayar da martani ne ga wulakanta kur'ani mai tsarki da aka yi a wasu kasashen turai a 'yan lokutan baya-bayan nan.

نمایش باشکوه قرآن در موکب اربعینی در کربلا + عکس

نمایش باشکوه قرآن در موکب اربعینی در کربلا + عکس

نمایش باشکوه قرآن در موکب اربعینی در کربلا + عکس

نمایش باشکوه قرآن در موکب اربعینی در کربلا + عکس

 

4167227

 

 

 

captcha