IQNA

Maukibin Kiristoci Masu Hidima Ga Masu ziyarar Arbaeen

17:08 - September 06, 2023
Lambar Labari: 3489772
Karbala (IQNA) Tawagar Kirista ta yi hidima ga masu ziyarar Arbaeen na Imam Hussain (AS) tare da musulmi.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na U News cewa, jerin gwanon mabiya addinin kirista mai taken “Soyayyar Husaini ta hada mu wuri daya” na shiga cikin hidima ga masu ziyarar Arbaeen.

Haka nan akwai jerin gwanon kiristoci a kan hanyar da masu ziyara Arbaeen suka yi tsakanin Najaf da Karbala, wanda ke cike da jerin gwano daga kasashen duniya daban-daban da addinai daban-daban, kuma dukkaninsu suna gudanar da hidima ga masu ziyarar Imam Hussain (a.s.) da dan uwansa Abul Fazl al-Abbas (a.s.).

Wannan tattaki mai taken "Soyayyar Husaini ta hada mu tare" ya hada da Kiristoci da Musulmai da dama da ke hidimar Arba'in da kuma samar da abinci da abin sha da sauran ababen bukatar rayuwa.

Miliyoyin al'ummar musulmi a fadin duniya na gudanar da tarukan  Arba'in, wanda ya kasance rana ta 40 da shahadar Imam Hussain (AS) da sahabbansa a ranar Ashura.

Arbaeen na Imam Husaini (AS) ana daukarsa a matsayin mafi girman al’amari a duniya, kuma a lokacinsa ne ake gudanar da tattaki na juyayi da makokin miliyoyin jama’a daga kasar Iraki da ma duniya baki daya suna zuwa kasar Karbala domin ziyartar hubbaren Imam Hussain (AS) da saurarn zuriyar manzon Allah (SAW) da suka yi shahada tare da shi a ranar Ashura.

 

4167232

 

captcha