IQNA

Koyar da littafan karatun Alqur'ani ta hanyar yanar gizo a Masar

14:38 - November 18, 2023
Lambar Labari: 3490167
Alkahira (IQNA) Cibiyar Musulunci ta Al-Azhar ta kasar Masar ta sanar da kaddamar da kwas din koyar da karatun kur'ani mai tsarki a karon farko a kasar ta hanayar yanar gizo.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Siddi al-Balad cewa, sashen kula da cibiyoyin Azhar ya sanar da fara karatun kur’ani mai tsarki a karon farko a duk fadin kasar Masar ta hanyar yanar gizo.

An kaddamar da wannan horon ne bisa la’akari da manufofin Ahmed Tayyeb Sheikh na Azhar da kuma karkashin kulawar Ayman Mohammad Abdul Ghani, shugaban Sashen Al-Azhar da kuma hadin gwiwa da Babban Darakta na Al-Azhar. -Azhar Computer.

A cewar Mohammad Abdul Ghani, shugaban sashen kula da cibiyoyin Azhar, an gudanar da wadannan tarurrukan ne bisa tsarin manufofin Azhar gaba daya na bunkasa harkar ilimi musamman fadada ilmummukan kur’ani.

Ya kara da cewa: Wannan shiri na ilimi na zahiri zai kasance ta hanyar kafar yada labarai ta ilimi a sashin cibiyoyin Azhar na YouTube da kuma shafin cibiyar Azhar, kuma masu sha'awar za su iya bin karantarwar littafan kur'ani ta wadannan shafuka. .

Abdul Ghani ya fayyace cewa: Wannan shiri na ilmantarwa ya kunshi bayanin dukkan ka'idoji da hukunce-hukuncen da suka shafi karatu da littafan tajwidi, da kuma misalai da aikace aikace na wadannan ka'idoji da hukunce-hukunce.

Ya kara da cewa: Za a gudanar da wannan shiri na ilimantarwa ne tare da hadin gwiwar wasu manyan malamai da karatun kur'ani a karkashin kulawar Abdul Karim Saleh shugaban kwamitin gudanarwa da sa ido kan bugu da karatun kur'ani mai tsarki a kasar Masar.

 

4182523

 

captcha