IQNA

Masallatan Morocco; Majagaba a yaki da jahilci

17:01 - December 01, 2023
Lambar Labari: 3490237
Rabat (IQNA) Ministan Awkaf na kasar Morocco ya sanar da halartar masallatai sama da 3,390 a yankunan karkarar kasar a cikin shirin yaki da jahilci.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na 24 Saed cewa, Ahmed Al-Tawfiq ministan ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci na kasar Maroko a cikin wani rahoto da ya aikewa majalisar dattijan kasar ya sanar da halartar masallatan Moroko da dama a cikin shirin yaki da jahilci.

A cewarsa, adadin mutanen da aka sanya a cikin shirin karatu a kauyukan kasar nan a shekarar karatu ta 2022-2023 sun kai mutane 137,592, wato kashi 47% na dukkan mutanen da suka shiga cikin wannan shirin.

A cewarsa, masallatan kasar Morocco sun taka rawa wajen yaki da jahilci, kuma tun bayan kaddamar da wannan shiri a shekara ta 2000, sama da mutane miliyan 4.5 ne suka yi amfani da wannan shirin a masallatai, wanda sama da mutane 1,875,000, wato kusan kashi 42% daga cikin wadannan mutanen, sun fito daga karkara.

Al-Tawfiq ya ce adadin masallatan da suka dauki nauyin karatun karatu a yankunan karkara sun kai masallatai 3391. Ya kuma sanar da karbuwar shirye-shiryen karatun boko da azuzuwan da mata ke yi a makarantu a yankunan karkara na kasar Maroko.

Ministan na kasar Morocco ya sanar da ci gaba da farfado da makarantun kur’ani a masallatan kasar nan ba da dadewa ba. Wadannan makarantu sun kasance cibiyar ilimi a birane da karkara a Maroko shekaru aru-aru.

 

4184883

 

captcha