Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-Masri Al-Youm cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta gudanar da wani shiri na mako-mako na taron karshe na kur’ani mai tsarki tare da sharhin warsh na Nafee, tare da halartar manyan makaratun Masar da kuma mahalarta daga kasashe 65 a gasar kur'ani ta duniya karo na 30.
Mohammad Mokhtar Juma, ministan ma’aikatar, a jawabinsa na jiya, 4 ga watan Disamba, ya jaddada cewa aikinmu shi ne kokarin karanta kur’ani mai tsarki a kowane gida da kuma ko’ina a cikin kasar Masar.