IQNA

Tare da halartar wakiliyar Iran;

A gobe ne za a bude gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Jordan

21:54 - February 16, 2024
Lambar Labari: 3490648
IQNA - A gobe ne za a gudanar da bikin bude gasar haddar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na 18 a kasar Jordan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-Dastur ta kasar Jordan cewa, za a gudanar da wadannan gasa ne a karkashin kulawar ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci a kasar Jordan, kuma za a ci gaba da gudanar da gasar har zuwa mako mai zuwa.

Mai magana da yawun ma'aikatar kula da harkokin jin kai ta kasar Jordan Ali Al-Daqamseh ya fitar da sanarwar manema labarai inda ya sanar da cewa: Za a gudanar da gasar haddar kur'ani mai tsarki ta Al-Hashmiyyeh karo na 18 daga ranar 17 zuwa 22 ga watan Fabrairu An bayyana a cikin wannan sanarwa cewa: A ranar Alhamis ne za a gudanar da bikin rufe gasar tare da karrama matan da suka yi fice a gasar a matsayin wani gagarumin biki da ma’aikatar bayar da tallafi za ta yi.

Abin tunatarwa ne cewa Zahra Abbasi Hafiz-e-Kol kur'ani kuma dalibar harshen larabci da adabin larabci a jami'ar Tehran ta kasance wakiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin wadannan gasa.

4200123

 

captcha