IQNA

Ana samun karuwar rashin amincewa da nuan wariya ta addini ga musulmia kasar faransa

18:39 - April 19, 2024
Lambar Labari: 3491010
IQNA - Jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta nanata a cikin wani rahoto da ta fitar cewa, a karkashin tasirin abubuwan da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, Musulman Faransa ba su ji dadin yadda ake nuna musu kyama ba.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta yi tsokaci kan halin da musulmi da larabawan Faransa suke ciki a wannan kasa. Wadanda, duk da rashin sanin juna, duk suna bayyana ra'ayi iri ɗaya kamar tsoro, rashin taimako, fushi da bakin ciki. 

A cikin wannan rahoto, an bayyana cewa, wadanda aka zanta da su, duk da sukar da suke yi kan halin da ake ciki, sun damu da cewa za a yi musu tsangwama, don haka ne suka ji tsoron kada a ambaci sunayensu a cikin rahoton.
Wadanda aka zanta da su sun jaddada cewa abubuwan da ke faruwa a yankunan Falasdinawa da aka mamaye bayan farmakin guguwar Al-Aqsa wani sabon salo ne na rashin aminta da al'ummar Faransa.

A zantawar da Musulman Faransa suka yi da Le Monde, sun yi Allah wadai da jawaban siyasa da kafafen yada labarai da ake yi a kansu da kuma yanayi mai daure kai da aka yi musu, inda suka jaddada cewa a yanzu sun zama 'yan kasa da wadanda abin ya shafa ke fuskantar matsaloli da dama da ba za a iya magance su ba.

A cikin rahoton da jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta fitar, an jaddada cewa da yawa daga cikin larabawa a kasar ta Faransa duk da cewa kakanninsu na kasar Faransa ne kuma ba sa jin harshen Larabci, suna fuskantar wariya da ya sanya suke tunanin barin Faransa.

Marubucin Le Monde ya yi nuni da cewa, abubuwan da suka faru na Charlie Hebdo, Hyper Kashre, da Bataclan a shekarar 2015 sun kasance wani sauyi ga wadannan ‘yan kasar Faransa musulmi, kuma a dunkule, bayan waki’ar ranar 11 ga Satumba, 2001, ra’ayoyin kasashen yammacin duniya kan musulmi sun canja.

 

4211220

 

captcha