IQNA

Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada wajabcin rage tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya

14:33 - April 20, 2024
Lambar Labari: 3491014
IQNA - Mataimakin kakakin babban sakataren MDD ya jaddada bukatar rage zaman dar-dar a yankin gabas ta tsakiya yana mai cewa: MDD na son dakatar da duk wasu matakan ramuwar gayya tare da neman dukkan bangarorin da su yi taka-tsantsan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Sama na  Falasdinu cewa, Farhan Haq a madadin babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa: Muna watsi da matakan mayar da martani, muna kuma gargadin kasashen yankin gabas ta tsakiya kan illar da ke tattare da tashe-tashen hankula.

Mataimakin kakakin babban magatakardar MDD ya bayyana cewa: Sakatare Janar na MDD ya yi la'akari da hanyar da za a bi wajen rage zaman dar-dar a tattaunawar da bangarorin biyu [Isra'ila] da Falasdinu ke yi da kuma tattaunawa kan samar da kasashe biyu.

Farhan Haq ya bayyana cewa, MDD na son dakatar da duk wasu matakan ramuwar gayya tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su yi taka-tsantsan tare da jaddada cewa: bala'in jin kai a Gaza ba a taba ganin irinsa ba, kuma muna bukatar karin taimako da za a aike wa Falasdinawa.

Ya kara da cewa: Babu wani ci gaba a fannin isar kayan agaji, don haka muna bukatar karin hadin kai domin kai kayan agaji zuwa arewacin Gaza.

Farhan Haq, yayin da yake jaddada wajabcin tsagaita bude wuta a Gaza, ya bukaci a kawar da duk wani cikas kan hanyar aika da kai kayan agaji ga al'ummar Gaza.

Yakin Gaza ya shiga kwana na 197, kuma ya zuwa yanzu mutane 34,012 suka yi shahada, kuma babu labarin tsagaita bude wuta.

Sojojin yahudawan sahyoniya na ci gaba da kai munanan hare-hare a zirin Gaza, kuma mutane da dama ne ke shahada da jikkata sakamakon wadannan hare-hare a kowace rana.

Bisa kididdigar da ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar, mutane 34,012 ne suka yi shahada yayin da mutane 76,833 suka jikkata a zirin Gaza tun farkon yakin. Adadin yaran da suka yi shahada ya zarce 14,000 sannan sama da mata 10,000 ne suka yi shahada.

 

4211347

 

 

 

captcha