IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Hadarin Da Masallacin Aqsa Ke Ciki

22:35 - October 08, 2016
Lambar Labari: 3480837
Bangaren kasa da kasa, A taron shugabannin kungiyoyin musulmia birnin Istanbul na Turkiya an jaddada cewa masallacin Aqsa mai alfarma yana fuskantar gagarumar barazana daga yahudawan sahyuniya.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na Anatoly ya bayar da rahoton cewa, taron wanda aka fara gudanarwa a jiya ya samu halartar malamai da masana fiye da 500 daga kasashe kimanin 30 na duniya.

Babban abin da taron ya mayar da hankali a kansa dai shi ne halin da masallacin aqsa mai alfarma yake ciki sakamakon keta alfarmarsa da yahudawan sahyuniya suke yi dare da rana, inda dukkanin mahalrta taron suka cimma matsaya a kan wajabcin kare wannan wuri mai tsarki.

Mahalrta taron sun bayyana cin zarafin musulmi Palastinawa da yahudawan sahyuniya ke yi a birnin quds da sauran yankunan palastinawa a matsayin cin zarafin dan adam wanda duniya ta yi gum da bakinta a kansa.

A kan haka malaman da kuma masana sun dora alhakin abin da yake faruwa a kna wuyayen manyan kasashen duniya da suke da ikon takawa haramtacciyar kasar Isra'ila burki kan cin zarafin palastinawa da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki na al'ummar musu7lmi da ma na kiristoci wanda yahudawa masu tsatsauran ra'ayi ke yi.

Ana gudanar da irin wannan taro a kowace shekara, wanda gwamnatin Turkiya ke daukar nauyinsa, amma a wannan karon taron ya samu halartar malamai da masana fiye da sauran lokutan baya.

3536402


captcha