IQNA

Fadar White House Ta Rusa Al'adar Taron Idin Karama Salla

22:44 - June 25, 2017
Lambar Labari: 3481643
Bangaren kasa da kasa, bisa ga al'ada ta tsawon shekaru kimanin 20 ana gudanar da taron idin karamar salla a cikin fadar white house amma wannan gwamnatin Amurka ta kawo karshen wannan al'ada.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar CNN ta bayar da rahoton cewa, Donald Trump tare da matarsa sun fitar da bayanin taya musulmi murnar taya musulmi kammala azumin watan Ramadan, amma ba su sanar da gayyatarsu zuwa fadar white house domin taron idi ba.

Rashin gayyatar musulmi zuwa taron idi a fadar white house bai zo ma musulmin Amurka da wani abin ban mamaki ba, domin a cewar da dama daga cikin musulmin Amurka, koda Trump ya yi gayyata da wahala a samu wanda zai halarci wurin daga cikin musulmi.

An fara gudanar da taron salla karama a cikin fadar white house ne tuna cikin shekara ta 1996 a lokacin mulkin Bill Clinton, wanda ya gayyaci msuulmi domin taron idi, daga nan kuma lamarin ya ci gaba har zuwa shekarar da ta gabata alokacin mulkin Obama.

A cikin shekara ta 1805 ne dai aka fara gayyatar wani musulmi zuwa buda baki a cikin fadar white house a lokacin shugabancin Thomas Jiffereson, wanda ya gayyaci jakadan kasar Tunisia.

Tun a lokacin yakin neman zaben Trump ne ya fito fili ya nuna irin kiyayyar da yake da ita akan musulmi da addinin muslunci, duk kuwa da cewa ya hada baki da wasu daga cikin musulmin da Amurka ke sayarwa makamai na biliyoyin kudi domin cutar da kasashen musulmi.

3613219


captcha