IQNA

Wani Mutum Ya Taka Musulmi Da Mota A Birnin New Castle

20:07 - June 26, 2017
Lambar Labari: 3481646
Bangaren kasa da kasa, wani mtum a cikin wata mota ya taka musulmi a ranar idia birnin Castle na Birtaniya da mota.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Star cewa, bayan kammala sallar idin karamar salla a jiya a birnin News Castle na kasar Birtaniya an kammadar da hari a kan da mota akan musulmi.

Wani mutum dan shekaru kimanin 42 ne ya kai harin, inda ya taka musulmi da mota tare da jikkata wasu daga cikinsu, nan take dai jami’an tsaron sun kame shi, sai sun ce harin bashi da alaka da ta’addanci, amma dai suna gudanar da bincike.

Irin wannan hari ya faru a cikin wannan mako a birnin London, inda wani mutum ya taka musulmi bayan sun kammala salla suna fitowa daga cikin masallaci, inda ya kasha tare da jikkata wasu.

Kasar Birtniya na daga cikin kasashen turai da a halin yanzu musulmi musulmi suke fuskantar barazana daga ‘yan kasar wadanda ba msulmi ba.

3613364


captcha