IQNA

Kotun Kolin Amurka Ta Amince Da Dokar Trump Kan Hana Musulmi Shiga Kasar

16:40 - June 27, 2017
Lambar Labari: 3481648
Bangaren kasa da kasa, Kotun koli a Amurka ta amince da aiwatar da wasu dokokin na shugaban kasar Donal Trump na hana baki daga wasu kasashen musulmi shiga kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kotun ta amince da dokar ne bayan da wasu kotuna suka ki amincewa da ita, tuni Donald Trump ya nuna farin ciki game da wannan hukunci, wanda aka jima ana takaddama a kai.

Mista Trump ya bayyana cewa hukuncin ya yi daidai da bukatar inganta harkan tsaron kasar, wanda a cewarsahakan ya nuna za'a jingine barin 'yan kasashe shida da ake kallon na da hatsari shiga Amurka saboda ta'addanci.

Hukuncin da kotun ta yanke da gagarimin rinjaye ya dai tanadi hana musulmi na kasashe shiga galibi musulmi da suka hada da Siriya, Iran, Sudan, Somaliya da Yemen sanya kafa a Amurka na wani dan lokaci.

Matakin dai ya tanadi hana duk wani dan tahaliki daga wadanda kasahen wandahukumomin Amurka basu da masaniya akan shi shiga Amurka.

3613562


captcha