IQNA

Shirin Bada Horo Kan Hardar Kur’ani ga Mata A Karbala

23:49 - June 28, 2017
Lambar Labari: 3481650
Bangaren kasa da kasa, an fara rijistar sunayen mata masu bukatar shiga cikin shirin bayar da horo kan hardar kur’ani mai tsarki a Karbala.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ,a ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hubbaren Hussaini cewa, an fara shirye-shiryen gudanar da shirin bayar da horo na hardar kur’ani a cikin bazara a karkashin wannan hubbare mai alfarma.

Malama Intesar Fadel wadda it ace mai kula da wannan shiri ta bayyana cewa, shekaru hudu kenan a jere da ake gudanar da wannan shiri ba tare da an dakatar ba, kuma yana ci gaba da kara samun karbuwa yadda ya kamata atsakanin mata a Iraki.

Ta ci gaba da cewa babbar manufar shirin dai it ace kara karfafa gwiwar mata kan lamarin kur’ani mai tsarki, musamman ganin yadda a lokutan nan ana samun ci gaba ta fuska, inda mata kan mayar da hankali a kan lamarin kur’ani a dukkanin bangarori.

Daga cikin abubwan da ake koyarwa dai har da karatu da kuma harda, gami da kaidojin karatun kur’ani mai tsarki,wanda hakan yake bayar da dama ga mata su iya koyar da wasu akalla iyalansu da ‘ya’yansu.

3613653


captcha