IQNA

Muhammad Jawad Zarif:

Ina Fatan Tattaunawar Kasashen Musulmi A Istanbul Ta Haifar Da Da Mai Ido

23:56 - August 02, 2017
Lambar Labari: 3481761
Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad zarif ya bayyana cewa, yana fatan zaman da kasashen msuulmi suka gudanar a birnin Istanbul na kasar Turkiya Palastinu ya haifar da da mai ido.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren diflomasiyya na ma’ikatar harkokin wajen Iran cewa, Muhammad Jawad Zarif ministan harkokin wajen Iran wanda ya halarci zaman da ministocin harkokin wajen kasashen msuulmis uka gudanar a Turkiya, ya bayyana fatan ganin zaman ya yi alfanu wajen taimakon al’ummar Palastine.

Zarif ya bayyana cewa, an jima ana gudanar da taruka akan halin da al’ummar Palastinu suke ciki dangane da zaluncin da suke fuskanta daga yahudawan sahyuniya ‘yan mamaya, amma abin takaici akan tashi ba tare da al’ummar Palastinu sun ga wani kasa daga kasashen msuulmi ba.

Daga karshe ya mika kiransa ga dukkanin wadanda suke da ruwa da tsaki da kuma damar taka rawa wajen ganin an takawa yahudawa birki, da su sauke nauyin da ke kansu wajen taimaka al’ummar Palastinu da kuma kare wurare masu tsarki da ake ke keta alfarmarsu.

3625738


captcha