IQNA

An Raba Littafi Mai Bayani Kan Aikin Hajji Ga Maniyyata Na Masar

23:41 - August 12, 2017
Lambar Labari: 3481790
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar alhazan kasar Masar ta sanar da cewa, an buga tare da raba wani littafi wanda yake yin bayani da kuma hannunka mai sanda ga mahajjatan kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babbar cibiyar addini ta Azhar ce ta dauki nauyin rubutawa da buga wannan littafi wanda ya kunshi bayanai da suka danganci aikin haji.

Muhyiddin Afifi shi ne babban darakta na cibiyar bincike da buga littafai a cibiyar Azahar, ya bayyana cewa sun buga wannan littafin ne da nufin kara wayar da kan maniyyata dangane da muhimman lamurra da suka danganci akikin haji wadanda ya kamata mai aikin hajji ya kiyaye su.

Baya ga haka kuma an nusantar da maniyyata kan muhimamncin kiyaye kaidoji da addini ba tare da wuwce gona da irio ba a cikin dukkanin lamari da ya shafi addinin msulucni aikin hajji ne ko ba aikin hajji ba.

Tun kafin alhazan Masar su fara tashi an yi musu bayani daga malamai daban-daban kamar yadda aka saba yi, bayan haka kuma aka hada kowanne su da kwafi guda na wannan littafi domin ya zame musu mai jagora.

Cibiyar Azhar dai tana nuna takaici matuka a kan duk wani abin da ke bata sunan muslucni na wuce gona da iri a cikin addini, wanda hakan yana daga cikina bubuwan da suke haifar da ta’addanci da sunan addinin muslunci wanda hakan yake samo tushe daga akidar wahabiyanci da kuma koyarwarta.

3629332


captcha