IQNA

Karshen Shekarar Karatu A Babbar Makarantar Kur’ani A Senegal

23:44 - August 14, 2017
Lambar Labari: 3481796
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taro na shekara-shekara da ake gudanarwa na karshen shekarar karatu a makarantar kur’ani mafi girma aSenegal.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren sadarwa na cibiya yada ala’dun muslucni cewa, a jiya an gudanar da taron kammala karatun shekara a cibiyar Darul Kur’an Kuki a garin Luga mai tazarar kilo mita 200 daga fadar mulkin kasar Senegal.

Wannan cibiya dai ta hada da makarantar kur’ani da kuma babban dakin karatu, wanda ya kunsi dubban littafai na ilimin addinin muslunci.

Sayyid Hassan Ismati shugaban ofishin kula da harkokin al’adun muslunci na ja mhuriyar musulunci ta Iran a Senegal, tare da was daga cikin manyan malamai na kasar sun halarci wurin wannan taro.

Darul Kur’an Kuki ita ce cibiyar muslunci da take da dakin karatu mafi girma a kasar Senegal, an kafa cibiyar ne tun kimanin shekaru 77 da suka gabata,a halin yanzu kuam tana da mahardata da makaranta kur’ani fiye da dubu hudu.

3630229


captcha