An gina wannan masallacin nea cikin shekara ta 1456 bayan rusa majami'oin basilica da mayakan dauar Usmaniya suka yia cikin Girka.
A cikin tsawon shekaru yaki da mayakan daular Usamniyya da kuma al'ummar Girka, an sake mayar da shi zuwa majami'a, amma a cikin shekara ta 1824, an mayar da wannan masallaci makaranta, bayan samun 'yancin kai a Girka, an mayar da wannan masallacia matsayin gidan kaso na sojoji, daga bisani kuma ya koma gidan biredi na sojoji.
A farkon karni na ashirin, an mayar da wannan masallaci wurin bincike na ilimi da kuma adana wasu daga cikin kayan tarihin kasar, a shekara ta 2010, an bayar da aikin gyaransa wanda aka kammala a halin yanzu, kuma ministan raya al'adu na kasar zai jagoranci bude shi.