IQNA

Karuwar Kymaar Musulmi A Kasar Australia

22:52 - January 22, 2018
Lambar Labari: 3482324
Bangaren kasa da kasa, an samu karuwar kyamar musulmi a cikin kasar Australiaa cikin shekarun baya-bayan nan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Daily Mial cewa, Ratib Junaid shugaban majlaisar musulmin kasar Australia ya bayyana cewa, cikin shekarun baya-bayan nan an samu karuwar kyamar musulmi a cikin kasar Australia.

Ya ci gaba da cewa wannan lamari yana faruwa nea  cikin shekaru goma na karshen nan, inda shekarar da ta gabata lamarin yafi muni fiye da sauran shekarun da ska gabata.

Daga cikin irin matsalolin da musulmi suke fuskanta har yin kalaman batunci a gare su a lokacin da suke gudanar da lamurransu an yau da kullum tare da sauran jama'a, wadanda akasarinsu ba musulmi ba ne.

Baya ga haka kuma wasu lokuta lamarin har yakan kai ga tozarta mata masu sanye da lullubi, wadanda an fi saurin gane cewa musulmi nea  duk lokacin da suka shiga cikin jama'a.

Shugaban majlaisar musulmin kasar Australia ya ce dole ne gwamnati ta dauki alhakin kare rayuka da mutuncin dukkanin 'yan kasa, wannan kuma ya hada har da musulmin kasar, domin suma yan kasa ne masu hakki kamar kowa a kasar.

Haka nan kuma ya kara da cewa, rashin daukar wani mataki kan wannan lamari, zai zubar da mutunci kasar a idon duniya, musamman kasantuwar kasar tana daga cikin masu da'awar dimukradiya da karbar dukkanin 'yan adam masu ambanbantan addinai da akidu.

3684226

 

captcha