IQNA

Rouhani: Kisan Khashoggi Jarabawa Ce Ga Masu Da’awa Kare Hakkin Dan Adam

22:24 - October 24, 2018
Lambar Labari: 3483070
Bangaren kasa da kasa, shugaban Iran Hasan Rouhani yayi Allah wadai da kisan gillan da aka yi wa Jamal Khashoggi tare da bayyana hakan a matsayin jarabawa ga masu da’awar kae hakkin dan adam a duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani yayi Allah wadai da kisan gillan da aka yi wa Jamal Khashoggi, sanannan dan jaridar kasar Saudiyyan nan yana mai bayyana cewar kisan gillan da aka yi masa wata babbar jarabawa ce ga masu ikirarin kare hakkokin bil'adama.

Shugaba Rouhanin ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi yayin taron 'yan majalisar ministocinsa a yau Laraba, inda ya ce kisan gillan da aka yi wa Khashoggin wani lamari ne mai tada hankali, wanda babu yadda za a yi kasar da ta aikata wannan danyen aikin ta aikata hakan ba tare da goyon bayan Amurka ba.

Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa: Aikata wannan danyen aikin wani lamari ne da ke nuni da irin yadda wata kautacciyar akida za ta iya haifar da matsala. Irin wannan akidar kuwa ita ce ta haifar da kungiyoyin ta'addanci irin su Daesh a yankin Gabas ta tsakiya. Don haka sai yayi kira da a gudanar da bincike na kasa da kasa mai cin gashin kansa don gano hakikanin abin da ya faru da kuma wadanda suke da hannu ciki don a hukunta su.

A ranar 2 ga watan Oktoban nan ne dai wasu jami'an tsaron Saudiyya da aka tura su kasar Turkey suka kashe Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Istanbul na kasar Turkey bayan da yaje can din don karbar wasu takardun da za su ba shi damar yin aure a kasar ta Turkiyya.

3758543

 

 

captcha