Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kakakin rundunar Haftar Ahmad Al-mismari ya fadi jiya cewa, mayakansu na ci gaba da kara nausawa a cikin birnin, kuma suna kwace muhimman wurare, da hakan ya hada da yankin Salahuddin da ke birnin.
Ya kara da cewa, kwace muhimamn wurare zai taimaka musu wajen kammala kwace birnin cikin kankanin lokaci a nan gaba.
Shedun gani da ido sun ce ana matsanancin gumurzu tsakanin dakarun gwamnatin Libya, da kuma dakarun Haftar a yunkurin da suke yi an kwace iko da barin sojoji dake yankin Yarmuk a gefen birnin Tripoli, da kuma babban kwalejin ‘yan sanda , da kuma ofishin hukumar kula da shige ta fice ta kasar.
Aftar dai yana samun dauki ne da taimako daga kasashen Saudiyya, UAE da kuma Faransa, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump yana daga cikin masu mara masa baya.