Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Birmingham mail ya bayar da rahoton cewa, a jiya an bude cibiyar koyar da kur'ani a birnin Birmingham, domin gudanar da ayyuka da suka shafi kur'ani.
Wannan cibiya za ta kunshi bangarori daban-daban da za su kasance wuraren bayar da karatu da suka hada da ajujuwa guda shida, da kuma wurin taro gami da masallaci.
Tun a shekara ta 1993 aka kafa cibiyar (QAF) da ke kula da lamurran kur'ani mai tsarkia kasar ta Birtaniya.
Masu kula da sabuwar cibiyar sun ce baya ga ilmomin kur'ani mai tsarki, za a rika koyar da wasu ilmomi na addini da kuma adabin larabci a wurin.