IQNA

An Fara Yin Salla A Kan Rufin Masallacin Manzon Allah (SAW) Saboda Yanayi Na Corona

22:27 - January 01, 2021
Lambar Labari: 3485515
Tehran (IQNA) an bayar da izini ga masallata kan su yi salla a kan rufin masallacin ma’aiki (SAW) saboda yanayi na corona.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kwamitin kula da harkokin masallacin manzon Allah (SAW) a Madina, ya bayar da izini ga masallata kan su yi salla a kan rufin masallacin mai alfarma, saboda yanayin da ake ciki na corona.

Bayanin ya ce kasantuwar mutanen da suke halartar masallacin suna da yawa, da kuma wajabcin kiyaye tazara a tsakanin jama’a, wannan yasa ana bukatar wurin salla fiye da wanda ake da shi saboda yawan jama’a.

Wannan yasa an bayar da wanann dama, saboda rufin masallacin manzo zai iya daukar masallata akalla dubu 10 a lokaci guda.

Bayanin ya ce dukkanin mutanen da suke salla a cikin masallacin da kuma cikin haraba gami da kan rufin, dole ne su kiyaye dukkanin ka’idojin da aka kafa domin kaucewa kamuwa ko yada cutar corona.

 

3944756

 

 

captcha