IQNA

Yan Bindiga Sun Sace Masallata A Jihar Zamfara ta Najeriya

16:18 - September 03, 2022
Lambar Labari: 3487793
Tehran (IQNA) 'yan ta'adda sun sace masu sallar Juma'a a jihar zamfara ta Najeriya.

Yan bindiga dake garkuwa da mutane domin karbar diyya a Najeriya, sun kai hari a kauyen Zugu dake Jihar Zamfara inda suka kwahse mutane a Masallachin Juma’ar garin wadanda suka je domin sauke farali.

Rahotanni sun ce Yan bindigar sun isa garin ne da misalin karfe 1 na rana a kasa, inda suka fara tattara mutane a Kasuwa, kafin daga bisani suka wuce Masallachin Juma’a suka kwashe masu jiran liman domin sauke farali.

Wani shaidar gani da ido a garin ya tabbatar mana aukuwar lamarin, yayin da yace jami’an tsaro cikin motoci guda 2 suna isa Zugun inda suka dauki wasu mutane 3 dan taimaka musu bin sawun barayin.

Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar matsalar tsaro sakamakon yadda Yan bindiga suka mamaye ta suna kai hari akan mutanen garuruwa daban daban.

 

4082728

 

 

 

 

captcha