IQNA

An sake bude masallacin Zanjeli mai tarihi a Ankara

15:59 - December 16, 2022
Lambar Labari: 3488344
Tehran (IQNA) A jiya ne aka bude masallacin Zanjeli mai dimbin tarihi a birnin Ankara tare da halartar jami'an gwamnati da 'yan majalisar dokokin Turkiyya bayan kammala aikin gyare-gyare.

A cewar Anatoly, a jiya an sake bude kofofin masallacin Zanjeli mai dimbin tarihi ga masallata bayan an shafe shekaru biyu ana aikin gyarawa.

Ministan al'adu da yawon bude ido Mohammad Nouri Arsavi, da jami'an gwamnati da dama da kuma 'yan majalisar dokokin Turkiyya sun halarci bikin bude wannan masallaci.

An gudanar da sallar isha'i ne a gaban dimbin al'ummar kasar a cikin wannan masallaci mai cike da tarihi, wanda ya faro tun karni na 17.

An kammala aikin gyaran Masallacin Zanjali dake unguwar "Altindagh" a birnin Ankara cikin shekaru biyu karkashin kulawar babban ma'aikatar bayar da tallafi.

Muhammad Amin Sheikhul-Islam Osmani ne ya gina wannan masallaci daga Ankara tsakanin 1618-1689. Masallacin Zanjeli yana da tsarin gine-gine mai kusurwa hudu tare da rufin katako, kuma ana amfani da jan dutse da bulo na Ankara wajen gina shi. An mayar da wannan masallaci a shekarar 1879 bisa umarnin Mohammad Khurshid Pasha, gwamnan Ankara na lokacin. Akwai makarantar addini mai hawa biyu da aka gina da itace a harabar masallacin Zanjeli.

 

 

4107340

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masallaci tarihi gwamnati masallata bude
captcha